Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

Kiyaye kirgen wata

 #KIYAYE ƘIRGEN KWANAKIN WATAN SHA'ABAN SUNNAH CE TA MANZON ALLAH ﷺ



Malamai sukace;

*”Yana cikin Sunnar Manzon Allah ﷺ kiyaye kirgen kwanakin watan Sha’aban dan shiga cikin watan Ramadhan batare da wasu shakka ba ko kukonto ba,kuma anyi hani da samun sabanin hakan”*.


Daga Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tana cewa:

*”Manzon Allah ﷺ yana kokarin kiyaye kirgen kwanakin sha’aban dan shiga watan Ramadhan,sannan yana azumin watan Ramadhana ne idan anga wata”*

@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺪﺍﺭﻗﻄﻨﻲ ﺑﺈﺳﻨﺎﺩ ﺻﺤﻴﺢ.

Daga Abi Hurairata ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ عنه yana cewa:

“Manzon Allah ﷺ yana cewa:

*(Ku kiyaye kirgen watan Sha’aban dan watan Ramadhana)*

@ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ.


Awata ruwayar suna cewa:

*(Ku kiyaye kirgen kwanakin watan Sha’aban………)*

@ﺣﺴﻨﻪ ﺍﻷﻟﺒﺎﻧﻲ ﻓﻲ ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ‏( 678 ‏).


Acikin littafin

” ﺗﺤﻔﺔ ﺍﻷﺣﻮﺫﻱ ”

“ﺍﺑﻦ ﺣﺠﺮ رحمه الله:

Yana cewa:

*”Wannan hadisi yana bayanine akan mu yi kokari wajan kiyaye kwanakin watan sha’aban,mu kiyaye kirgensa tun daga farkon tsayuwar watan har zuwa karshensa dan magance sabanin kamawar watan Ramadhan,ta yadda baza’a sami sabani ba da rububa”*


Yazo acikin littafin

“ﺍﻟﻤﻮﺳﻮﻋﺔ ﺍﻟﻔﻘﻬﻴﺔ “‏(2223/ ‏)

*”Ganin wata da kiyaye kirgensa yana da alaqa da kiyaye wasu ibadu na masu muhimmanci,sai aka shar’antawa musulmai su kiyaye kwanaki dan samun shiga watan batare da banani ko samun ruduba……..”*


Allah ne mafi sani


*Karatun Hadisi da aiki da shi,shine zaman lafiyar Musulmai

Post a Comment

0 Comments