#MUTANE SUN KASU KASO BIYAR 5 GAME DA LADAR SALLAR SU
العلَّامة الإِمَامُ ابْنِ الْقَيِّــــمِ رَحِمــــَهُ الله تعالىٰ-:
Yana cewa:
"Mutane sun kasu kaso biyar 5 game da sallarsu da kuma matsayin sallarsu a wajan Allah:-
1-Mai laifi wanda Allah zaiyi masa Uquba saboda sallarsa.
Shine wanda baya cika sallarsa baya alwalar sallar ciakkiya kuma baya cika rukunan sallah baya cika wajiban sallar baya cika sharuddanta,yana yin sallar ne yanda yaga dama,sallarsa ta sabama irin Sallar Manzon Allah s.a.w, to mai irin wannan sallah Allah zaiyi masa uquba saboda sallarsa.
2-Wanda Allah zaiyi masa Hisabi akan sallarsa.
Shine wanda zaiyi sallah yazo da ita da rukunnanta da wajibanta da Sharuddanta,sai dai tun daga lokacin da aka kabbara sallar bai san ake cikiba har zuwa sallama,saboda zuciyarsa ta shiga tunani da shagala da tuniya ya manta ma sallah yake,da zaka tambayesa wani sura aka karanta bazai iya tunawa ba saboda zuciyarsa da tunaninsa basu cikin sallah,mai irin wannan sallah shine Allah zaiyi masa Hisabi akan sallarsa.
3-Akwai wanda Sallarsa take kankare masa laifukansa.
Shine wanda zai zo da sallarsa cikakkiya da rukunnanta da wajibanta da Sharuddanta cikakku,amma tun daga lokacin da ya shiga cikin sallar to yana cikin sauri da gaggawar yaga angama sallar,shaidhaninsa yana so ya karkatar da zuciyarsa amma yana kokarin yaki da zuciyarsa da shaidhan yaga ya maidao da hankalinsa gaba da akan sallarsa,mai irin wannan sallah shine Allah yake kankare masa laifunsa na tunanin da yake da saurin da yake acikin sallarsa,saboda jihadin da yayi na kokarin maido da zuciyarsa da tunaninsa cikin sallar.
4-Wanda yake dacewa da samun ladar sallarsa mai girma.
Shine wanda ya zo da sallarsa cikakkiya ta wajan rukunnanta da sharuddanta da wajibanta,da mustahabbanta tare da khushu'i da na zuciya dana gabbai ba tare da wani tunanin duniya ba acikin sallarsaba,to mai irin wannan sallah shine wanda Allah yake bashi ladar cikakkiyar sallarsa.
5-Wanda sallarsa take sanya ya sami kusanci da ita awajan Allah.
Wannan shine matsayin mai sallah mafi daukaka,shine wanda zaizo da sallarsa,cikakkiya ta wajan rukunnanta da sharuddanta da wajibanta,da mustahabbanta tare da khushu'i da na zuciya dana gabbai ba tare da wani tunanin duniya ba acikin sallarsaba tare da halarto Allah a zuciyarsa wato yana ganine na musamman da Allah zuciyarsa tana mai cike da tuna Allah da halartosa acikin sallarsa.
Dukkan wanda yazo da sallah wadda take dauke da sharudda da rukunnnai da wajibai da mustahabbai da khushu'i da cikakku tare da halarto Allah da tuna Allah da gani dashi kadai acikin sallarsa,kuma Allah yana kallonsa to hakika ya sami matsayi mafi daukaka daga cikin matsayin masu sallah,shine ya sami kusancin Allah ta dalilin wannan sallah tasa.
@الوَابِلُ الصَّيِّب ص"٤٠ - ٥٠ " لِاِبْنٍ الْقَيِّمِ الْجَوْزِيَّة.
Allah ne mafi sani.
Allah ka sanya musami kusanci zuwa gareka ta hanyar sallarmu.

0 Comments